Majalisar Ƙoli ta harkokin Shari'ar Musulunci ta Najeriya ce a ƙarƙashin shugabancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ta nemi a samar da dokokin da za su tantance masu wa'azi, lamarin da ya ja hankalin mutane.
Wannan kiran na sarkin ya zo daidai lokacin da al'ummar Musulmi suke fara gudanar da azumin watan Ramadan, lokacin da malamai suke gudanar da tafsiri da sauran karantarwa.
Dama tun a baya wasu malaman da shugabannin addinin Musulunci a Najeriya, sun daɗe suna bayyana cewa lokaci ya yi da za a samar da dokoki da suka shafi yadda ake gudanar da wa'azi a faɗin ƙasar.
Shin ya dace a samar da dokokin?
Yaya malamai suke kallon batun?
Yaya lauyoyi suke kallon wannan matakin?
Shin wane tasiri dokokin za su yi?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.
Comments
Leave a Comment