Fatar da ke kunshe da ruwa a jakar ƙwayayen mace wato 'ovarian cyst' a mafi yawancin lokuta, an fi gano shi ne a lokacin da aka yi hoton ciki.
A cewar masana fatar mai kama da jaka da ke ƙunshe da ruwa da kan fito a jakar kwan ɗaya ko duka biyu sun kasu zuwa gida biyu.
Kashi na farko shi ne mai sauƙi, wanda ƙarami ne kuma ya kan ɓace da kansa bayan wani lokaci, a don haka babu buƙatar yin komai sai dai a jira.
Sai dai idan ya girma sosai ko kuma ya murɗe, za a iya ɗaukar matakin cire shi ta hanyar tiyata.
Kashi na biyun kuma, ba ruwa kaɗai ke ƙunshe a cikin fatar ba, sannan ya kan fitar da sinadarai a kan mahaifa.
Wannan kashi na biyun na janyo wasu matsalolin da suka haɗa da zuban jini da ciwon ciki.
Dr. Hurera Umar ta asibitin Babbar Ruga a jihar Katsina da ke Najeriya ta yi cikakken bayani kan wannan matsala. Don haka latsa makunnin da ke sama domin sauraron shirin lafiya Zinariya.
Comments
Leave a Comment