Kano Pillars ta yi nasarar cin Rangers 2-1 a wasan mako na 27 a gasar Premier ta Najeriya a filin wasa na Sani Abacha a Kano.
An kusa yin hutu ne Rangers ta fara cin ƙwallo a bugun fenariti ta hannun Bashir Usman, sai dai minti tara tsakani Pillars ta farke ta hannun Rabi'u Ali.
Bayan da aka koma zagaye na biyu ne kuma wasa ya natsa, shi ne Pillars ta kara na biyu ta hannun Jerry Alex, hakan ya sa ta haɗa maki ukun da take bukata.
Da wannan sakamakon Pillars wadda ake kira sai masu gida ta koma ta huɗun teburi da maki 42, bayan wasan mako na 27 da cin karawa 12 da canjaras shida aka doke ta wasa tara.
Tornadoes 0-1 Enyimba
Bayelsa Utd 2-1 Bendel Insurance
Abia Warriors 1-1 Nasarawa Utd
Akwa United da Katsina United
El Kanemi Warriors da Lobi Stars
Shooting Stars da Rivers United
Comments
Leave a Comment