Barcelona ta koma kan teburin La Liga

Facebook Twitter LinkedIn
Barcelona ta koma kan teburin La Liga

Barcelona ta doke Real Sociedad 4-0 a wasan mako na 26 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi ta koma jan ragamar teburin La Liga.

Minti na 17 da fara wasa aka bai wa ɗan wasan Sociedad jan kati, wato Aritz Elustondo.

Kuma minti takwas tsakani Barcelona ta fara cin ƙwallo ta hannun Gerard Martín, haka kuma minti biyar tsakani Marc Casado ya kara na biyu.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Ronald Araújo ya kara na uku, sannan Robert Lewandowski ya zura na huɗu raga.

Da wannan sakamakon Barcelona ta koma matakin farko da maki 57, bayan cin wasa 18 da canjaras uku aka doke ta karawa biyar.

Atletico Madrid ce ta biyu da maki 56, saboda cin Athletic Club 1-0 ranar Asabar.

Ita kuwa Real Madrid mai maki 54 mai rike da kofin ta yi kasa zuwa ta ukun teburin La Liga, saboda doke ta 2-1 da Real Betis ta yi ranar Asabar.

Ranar Laraba 5 ga watan Maris Barcelona za ta je gidan Benfica a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League.

Wasan gaba da Barcelona za ta buga shi ne wanda za ta karɓi bakuncin Osasuna a wasan mako na 27 a La Liga ranar Asabar 8 ga watan Maris.

admin

admin

Content creator at LTD News. Passionate about delivering high-quality news and stories.

Comments

Leave a Comment

Be the first to comment on this article!
Loading...

Loading next article...

You've read all our articles!

Error loading more articles

loader